fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Ji halin ban tausai da marasa lafiya suka shiga yayin da Likitocin Najeriya suka fara yajin aiki, Gwamnati ta yi barazanar daukar mataki

Kungiyar Likitocin Najeriya ta NARD ta shiga yajin aiki duk da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin tarayya.

 

Hakan yasa asibitoci a jihohi da dama suka daina karbar marasa lafiya idan ba wanda ke cikin halin bukatar kulawar gaggawa ba.

 

Rahoton punchng ya bayyana cewa, mutane da yawa masara lafiyane suka ziyarci asibitoci yayin da aka fara yajin aikin amma babu Likitocin da zasu kula dasu. An rika ce musu su koma gida.

 

A Asibitin Kano, Rahoton ya Bayyana cewa, mutane sun rika dauke danginsu daga Asibitin Gwamnati saboda yajin aikin.

 

A matarnin gwamnati kan wannan lamarin, Ministan kwadago, Chris Ngige ya bayyana cewa, bai kamata ba abinda Likitocin suka yi. Yace ana maganar rayuwar jama’a ne, kuma zasu basu nan da zuwa karshe mako, idan basu jabasu janye yajin aikin ba, zasu dauki mataki.

“We have not reached that (no-work-no-pay) stage yet.  People’s lives are involved. Their own is not the same with teachers in universities who can claim that they will teach day and night to cover lost grounds.

“This one is that if you don’t treat a patient, the patient dies and you can’t bring the person back to life. If by this weekend, they are still pressing on with their strike, we will look at all the labour laws and the options available to government including but not limited to enterprise; the employers trying to protect their enterprise and the lives of their patients.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *