fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Ji irin wayon kananan yara da kawa Sunday Igboho aka kamashi

Lauyan Sunday Igboho yayi ikirarin cewa,  Sunday Igboho ne da kansa ya mika kansa wajan jami’an tsaro, amma Rahoton Punchng ya karyata hakan.

 

Rahoton yace Sunday Igboho ya je filin jirgin sama na kasar Benin Republic dan tserewa zuwa kasar Jamus da matarsa.

 

Saidai da abincike yayi zurfi, an gano cewa shine wanda ake nema ruwa a jallo a Najeriya sannan fasfonsa na cike da alamar tambaya.

 

Sunday Igboho da ya ga ana shirin ganoshi, sai ya sulale daga wajan, aka nemi sama ko kasa aka rasa.

 

Saidai washe gari, jami’an dake filin Jirgin saman sun Kira Igboho inda suka gaya masa cewa,  ya zo ya karbi Fasfon nashi dan an kammala binciken da za’a yi kuma ba’a samu wata matsala ba.

 

Saidai yana zuwa sai suka yi ram dashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *