fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Ji sabon matakin gamawa da ‘yan Biafra da Gwamnati zata dauka

Gwamnan jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Najeriya, David Umahi, ya yi barazanar kama iyayen ƴan awaren da ake zargi da kai hari kan fararen hula.

Gwamnan ya ce matakin zai kawo ƙarshen yawan tashin hankalin da ake yi yanzu a jihar ta Ebonyi.

Mista Umahi ya ce sarakunan gargajiya sun san ƴan bindigar da ke kai hare-haren da iyayen ƴan bindigar da kuma inda suke ɓuya, amma kuma sun ƙi tona su.

Yankin kudu maso gabashin Najeriya na fama da tashin hankali da ke ta ƙaruwa, wanda kuma ke da alaƙa da ƴan aware masu fafutukar kafa ƙasarsu ta Biafra.

Yayin da gwamnan na Ebonyi ke wannan barazana, gwamnatin tarayyar Najeriyar ta ce mai yuwuwa ta sanya dokar ta-ɓaci a jihar Anambra kafin zaɓen gwamnan jihar da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba, domin dakile tashe-tashen hankalin da ake yi a can.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *