fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Ji Sabon Sharrin da Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta kalawa Arewa

Kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayyana cewa matsalar rashin tsaron dake faruwa a yankinsu, Arewace ta shiryashi.

 

Kungiyar tace Arewa a shekarar 2015 ta samarwa kanta matsalar tsaro dan ace Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya gaza su kwace mulki a hannunshi.

 

Kungiyar ta kara da cewa, Shine a yanzu da shekarar 2023 ke karatowa, Inyamurai na ganin cewa zasu samu Shugabancin Najeriya, Arewa ta haddasa musu matsalar tsaro dan kawar da hankalinsu.

 

Kungiyar ta bayyana hakane cikin sakon martanin da tawa tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wammako kan cewar da yayi su daina kashe ‘yan Arewa da lalata dukiyarsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *