fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Ji wata makarkashiya da aka gano Atiku yawa shugaba Buhari

A shekarar 2018, bayan da ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiki Abubakar ya dauki hayar wani kamfanin kasar Amurka dan yiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari makarkashiya.

 

Peoplesgazette ta ruwaito cewa, Atiku ya biya sama da Biliyan 8 dan a lalata yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

 

A wancan lokacin an rika yayata cewa kasar Amurka ta hana Atiku Abubakar zuwa kasarta saboda zargin Almun dahana.

 

Rahoton yace Atiku ya baiwa kamfanin K.M. Family Investment, LLC na kasar Amurka aikin samar masa da Visa ta shiga kasar.

 

Kuma a wancan lokacin, Atiku Abubakar ya samu shiga kasar ta Amurka inda ya samu rakiyar Bukola Saraki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *