fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Ji wata Sabuwar mugunta da ‘yan Bindiga suka bullo da ita kan ‘yan Arewa

Manoma a wasu yankuna jihar Zamfara da ke fama da hare-haren ƴan bindiga masu fashi da satar mutane sun ce ƴan bindiga sun fara ƙona amfanin gonarsu.

Al’ummar yankin Magami a ƙaramar hukumar Gusau ta Zamfara sun ce wannan lamarin na ƙara jefa su cikin mummnan yanayi wanda ka iya janyo ƙarancin abinci.

Wani mazauni yankin da muka sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya shaida wa BBC cewa ƴan fashi sun sanya wa ƙauyukan yankin haraji, kuma matuƙar ba a biya ba, sukan matsa musu da sace duk mutanen da suka yi kasadar zuwa gona, ko ma su ƙone amfanin gonar.

“Yanzu bala’in da suka yi muna gona biyu suka cinna wa wuta ranar Litinin a Magami,” in ji shi.

Sai dai, rundunar ‘yan sandan jihar ta musanta bayanan ƙona amfanin gonar, inda ta ce ba a kai mata wani rahoto game da lamarin ba.

Kakakin rundunar ƴan sandan Zamfara SP Muhammad Shehu ya ce “hukumance ba mu samu wannan rahoton ba amma idan har akwai waɗanda suka yi ƙorafin sai su sanar da jami’an tsaro.”

A cewarsa an baza jami’an tsaro a sassan Zamfara kuma sun shaida wa al’umma cewa idan har suna fuskantar barazana su yi ƙoƙarin arin sanar da jami’an tsaro da ke kusa.

Amma wani Almustapha Abdullahi ya wallafa a Facebook inda yake iƙirarin cewa gonarsa ce ƴan bindiga suka shiga suka ƙone tare da yin garkuwa da mutane tare da wallafa hotunan gonar.

“Bayan baro garin Gusau da na yi, isowa gida ke da wuya (Magami ) na tarar da labarin yan ta’adda sun zo gonata wacce na noma masara, sun ƙone duka amfanin da masu aikin suka tara, Sannan sun yi garkuwa da masu aikin, mafi yawan masu aikin mata ne da kuma ƙananan yara,” kamar yadda ya bayyana a Facebook.

Mutanen Magami sun ce duk da akwai sojoji amma kuma a kullum ana tare hanya sau huɗu zuwa biyar a rana tare da tilasta masu biyan haraji.

Mazaunin yankin da BBC ta yi hira da shi ya ce ɓarayin sun ƙona gonakin ne lokacin da wasu manoma da suka haɗa da mata suka fita yin gurzar masara.

“Sun tafi da matan kafin daga baya suka sake su amma sun cinna wa gonar masarar wuta.”

“Sun kuma yi gargadin cewa idan ba a biya kudin da suka nema ba za su ci gaba da kona gonakin,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa yanzu haka mutanen gari sun tara kuɗi tsakaninsu da za su ba ƴan bindiga amma a cewarsa sukan hana manoma aiki har sai an biya su kuɗaɗen da suka nema.

Jihar Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar ƴan fashin daji masu satar mutane da hare-hare, kuma duk da matakan da hukumomi suka ɗauka da suka haɗa da toshe layukan sadarwa amma har yanzu ana ci gaba da kai hare-hare.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *