fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Ji yanda aka gano cocin da ake dirkawa mata ciki ana sayar da jariran

‘Yansanda a jihar Imo sun gano wata coci a Imo South wadda ake dirkawa mata ciki ana sayarwa da mutane jariran.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Michael Abattam yace sun fara bincike ne bayan da aka bayyana cewa, wata yarinya me shekaru 18,Amarachi Dioku ta bace.

 

An bayyana cewa an ga yarinyar a wata coci, inda kuma aka aika ‘yansanda suka gano cocin tare da kama mutane 5 dake cikinta.

 

Wadanda aka kama din sune, Ugochi Orisakwe ,me shekaru 47, sai Chidi Orisakwe , 34 , Pauline Nwagbunwanne , 42 , Elizabeth Uzoma,61 da Chibueze Joy ,31.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *