fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Ji yanda Mafusata suka babbake barawon mashin da ransa

Wasu mafusatan Matasa sun babbake barawon mashin da ransa a jihar Delta.

 

Lamarin ya farune da safiyar ranar Litinin wajan karfe 8:45 a yankin Afiesere na karamar hukumar Ughelli North.

 

Barawon ya kwace mashin dinne daga hannun maishi inda ya gudu, saidai kamin yayi nisa, Mai Mashin din ya kwarma Ihu inda mutane suka kawo masa dauki.

 

Da barawon ya ga ba zai tsira ba, sai ya yadda mashin din ya taka da gudu amma aka kamoshi aka masa dukan tsiya aka kuma konashi da ranshi, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *