fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Ji yanda Sojojin Najeriya sukawa Boko Haram kisan kiyashi

Wasu jiragen yakin sojin saman Najeriya sun dakile wani harin da kungiyar ISWAP ta shirya kai wa a garin Ngamdu mai iyaka da jihohin Yobe da Adamawa.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa baya ga Ngamdu maharan sun so kai hari a wani sansanin soji da ke yankin, kafin jiragen su yi musu luguden wuta.

Wata majiyar tsaro ta ce dama rundunar sojin Najeriya ta samu bayanan sirri cewa ISWAP na shirin kitsa hare-hare, kuma kungiyar ta tsara amfani da hanyar Goniri da Damboa don shiga Ngamdu.

Majiyar ta kara da cewa ” suna cikin tunkarowa ne sojoji suka bude musu wuta ta sama da kasa ta kashe su.”

Sai dai kawo yanzu babu sanarwar adadin mayakan ISWAP din da aka kashe a kwanton baunar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *