fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

JIBWIS Ta Yi Allah Wadai Da Wadanda Ke Alakanta Minista Sheik Pantami Da Kungiyar Ta’addanci

Kungiyar JIBWIS ta yi Allah wadai da masu jingina wa ministan sadarwa da tattalin arziki Sheikh Dr. Isa Ali Pantami laifin goyon bayan ta’addanci.

 

Kungiyar na biye da irin tattaunawar da ke gudana musamman a kafafen sadarwan zamani game da zargin da wasu masu neman tada zaune tsaye ke yi ma Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Najeriya wato Sheikh Dr. Isa Ali Pantami na cewa wai yana da ra’ayi irin na yan ta’adda kuma yana goyon bayan ta’addanci.

 

Babu ko shakka wannan zargi ne marar tushe wanda ke nuna jahilci ko rashin adalcin wadanda ke yin sa musamman in an duba abubuwa kamar

 

1. Sheikh Dr. Isa Ali Pantami Malami ne mai kira zuwa ga bin addinin musulunci bisa tafarkin Sunnar Manzon Allah (S.A.W.) , shi kuwa addinin musulunci bai yarda da ta’addanci ba ko zubar da jinanen mutane wadanda basu ji ba basu gani ba.

 

2. Duk wanda ya san Sheikh Pantami ya san cewa tsawon rayuwarsa babu abinda ya yi fada da shi irin aqidar tsatstsauran ra’ayin addini, wannan ne ma ya sa a lokutta daban daban malamin ya yi muqabala da wanda ya assasa kungiyar Boko Haram wato Muhammad Yusuf a bainal jama’a kuma ya kure shi da ingantattun hujjoji, akwai kasa-kasan bidiyon tattaunawar ta su hatta a kafafen sadarwa a yanzu haka ga duk mai son ya tabbatar.

 

3. Sauye-sauyen da Sheikh Pantami ya kawo a fagen sadarwa na Najeriya sun bada gudummawa matuka wurin karya lagon yan ta’adda wanda hakan ya sa suka yi ta aika masa da sakonni na barazanar kisa.

 

4. Dr. Pantami ya kawo sababbin tsare-tsare da suka taimaka wurin farfado da tattalin arzikin Najeriya tare da bashi kariya daga zagon kasan batattu da maciya hanci da rashawa.

 

Irin wadannan dalilan ne da makamantansu ke sa duk mai hankali zai tamabyi kansa cewa:

*Anya wannan bita da kulli da ake kokarin yi ma Sheikh Pantami ba wani salo ba ne na fada da addinin musulunci da wasu dibgaggu ke ganin cewa malaman addini komain musulunci komai kwarewarsu bai cancanta su rike mukamai na gwamnati masu muhimmanci ba irin wanda Sheikh Pantamin ke rike da shi a yayinda a gefe daya kuma basu ganin rashin cancantar hakan ga dimbin malaman wasu addinan da ke rike da mukamai iri daban daban a cikin madafun ikon kasar?

*Anya wadanda ke ganin cewa tsare-tsaren da Pantami ya kawo na dakile cin hanci da rashawa da dabaibaye ta’addanci ba su ne ke kokarin maida martini ba ta hanyar shafa Pantami kashin kaji don raba shi da mukaminsa?

*Anya babu siyasa da bangaranci da nuna wariyar addini cikin wadannan kiraye-kiraye na neman Sheikh Pantami ya yi murabus musamman in mun kalli tarihin wadanda ke yin kiraye-kirayen na neman tada zaune tsaye da alakokinsu da wasu manyan jagororin adawa da jam’iyyunsu?

*In har ana yin kiraye-kirayen ne saboda kishin Najeriya da damuwa da makomarta to me ya sa bamu ji muryoyin masu kiran ba wurin neman a dauki mataki a kan yan ta’addan da suka fito fili suna barazanar raba kasa tare da alkawarin kisa ga duk wanda bai basu goyon baya ba daga cikin jagororin yankinsu?

*Me ya sa basu yi Magana ba a lokacin da wasu yan ta’addan suka kutsa ofisoshin yan sanda a yankunansu suka yi ma yansanda kisan gilla suka saci makamai kuma suka kone ofisoshin?

A karshe Kungiyar Izala na kira ga yan Najeriya da su yi watsi da wannan zargi mara tushe, su kuma zamo masu adalci da son zaman lafiya da hakurin zama da juna.

Muna rokon Allah Ya zaunar da Najeriya lafiya, Ya yi riko da hannun jagororinta zuwa ga duk abinda yake maslaha ga kasa, Ya kuma kareta daga sharrin makiya.

Shugaban JIBWIS Naijeriya

Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *