fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Jihar Kaduna ta hana kasuwancin sayar da Gas din girki a cikin jama’a

Jihar Kaduna ta saka dokar hana kasuwancin sayar da Gas din girki a wuraren zaman mutane da kuma gurare masu hadari a jihar inda dokar zata fara amfani nan take.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kwamishinan kula da tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a sanarwar daya fitar inda ya bayyana cewa, duk me kasuwancin sayar da Gas din girkin dake tsakanin gidajen Al’umma ya rufeshi nan take.

Sanarwar ta kara da cewa an bukaci ma’aikatun dake da alhakin kula da kasuwanci masu hadari dasu sake duba dokar yin kasuwanci me hadari a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan da fashewar tukunyar Gas a Kaduna ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 ciki hadda shugaban hukumar kula da makamashin Atom ta kasa da dansa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *