fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Jihar Katsina na shirin mayar da gidajen Kallon Kwallo makarantun Islamiya

Majalisar Jihar Katsina ta fara shirin mayar da gidajen kallo makarantun Islamiya.

 

Dan majalisar, Mustapha Yusuf Jibia ne ya bayyana haka a zauren majalisar. Yace yawancin gidajen kallon an barsu sun zama kufai.

 

Sannan kuma ‘yan Bindiga na korafin cewa ‘ya’yansu basu da makarantun da suke zuwa.

 

Yace idan aka mayar da gidajen kallon makarantun Islamiya, zasu taimaka sosai wajan magance matsalar tsaro da kuma samarwa mutane aikin yi, dan gwamnati zata dauki malamai ta rika biyansu Albashi.

 

Majalisar ta kafa kwamiti na musamman da zai duba da kawo mata rahoto kan wannan bukata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *