fbpx
Monday, November 29
Shadow

Jihar Yobe: ‘Yan uwa sun guntule wa junansu hannu wajan fada

Faɗa ya kaure tsakanin wasu matasa biyu ƴan uwan juna a jihar Yoben Najeriya lamarin da ya yi sanadin kowane daga cikinsu ya rasa hannunsa na hagu.

Lamarin ya faru ne a garin Alkali da ke ƙaramar hukumar Dapchi ta jihar Yobe.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya shaida wa BBC cewa matasan – Bukar Audu da Bukar Muhammad – dukkansu ‘yan shekara 25, sun sari juna ne da adduna kuma suka guntule wa juna hannu kowane daga gaɓa.

Tuni dai ‘yan sanda suka karɓe hannuwan tare da kai su ajiya asibiti, da nufin gabatar da su matsayin shaida a gaban kotu.

ASP Dungus ya ce tun daga Nguru zuwa Gashua da Yunusari har zuwa yankin da lamarin ya faru akwai kogi a wurin wanda matasan yankin ke amfani da shi wajen noma da kiwo kuma akasari ana samun faɗa a tsakaninsu.

Ya ce makamancin irin faɗan ne aka yi tsakanin Bukar Audu da Bukar Muhammad kuma matasan duka suna asibiti suna jinya. Ya bayyana cewa saboda zafin ciwo ɗaya matashin ko magana ba ya iya yi amma ɗayan yakan ɗan yi bayanai.

ASP Dungus ya ce a halin yanzu babu cikakken bayani kan musabbabin wannan faɗa saboda dukannin matasan na cikin raɗaɗin ciwo, amma da zarar an samu kansu za a ci gaba da bincike.

Ya ce akan samu irin wannan ƙazamin faɗa, “akasari abin ya ta’alaƙƙa ne ko a kan dabbobi ko a kan ciyawa ko a kan ƙwaya ko a kan yarinya”.

A cewarsa kusan kashi hamsin bisa ɗari na irin waɗannan matasa suna ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Kakakin ‘yan sandan ya ce ba wannan ne karon farko da irin wannan lamari ya faru ba a yankin domin ko a kwanakin baya sai da wani yaro ya kashe mahaifinsa saboda abincin dabbobi.

Ya ce da suka yi bincike suka gano matashin na shan ƙwayoyi, wanda su ne suka sa ya rafka wa mahaifinsa sanda a kai.

Ya kara da cewa a yanzu haka suna ƙoƙarin ganin an samu jituwa tsakanin matasa a unguwanni da iyayen matasa haka kuma sun soma ɗaukar mataki kan irin taruwar da matasa ke yi babu dalili.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *