fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Jihar Zamfara na jiran matakin da za’a dauka kan Sojan da aka kama na kaiwa ‘yan Bindiga makamai

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce tana jiran matakin da sojoji za su dauka a kan wani jami’in Soja da aka kama tare da budurwarsa bisa zargin bai wa ’yan fashi bindigogi da kakin soja.

Mataimakin Shugaban Ma’aikata na Gidan Gwamnati, Dr. Bashir Muhammad Maru ya ce, Sojojin sun kame Jami’in Sojan ne da budurwar tasa.
Maru ya ce, “Wani batun mahimmin mahimmanci shi ne kame wani jami’in Soja da budurwarsa da ke taimakawa ‘yan fashi da kakin soji da alburusai cikin hadin gwiwa tare da sauran masu zagon kasa”.
“Yayin da gwamnatin jihar ke jiran matakin da sojoji za su dauka a kan wannan lamarin tare da yin bayani a hukumance, ci gaban ya kara tabbatar da matsayin Gwamna Bello Matawalle cewa matukar dai ba a tsarkake yakin da ake yi da‘ yan bindiga daga munanan kwayaye da masu zagon kasa ba, ba za mu sami nasarar da ake so a cikin yakin ba”.
Lokacin da aka tuntube shi, Hedkwatar Tsaro ta yi alkawarin bayar da sanarwa kan kamun amma har yanzu ba ta yi hakan ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *