fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Jihohin Arewa 7 sun Rufe Makarantu saboda fargabar tsaro

Akalla jihohin Arewa 7 ne suka Rufe Makarantu saboda fargabar tsaro a cikin watanni 2 da suka gabata.

 

Masana sun yi hasashen cewa hakan zai kara yawan yaran da basa zuwa Makaranta a Najeriya wanda a yanzu UNICEF ta sakashi a matsayin Yara Miliyan 10.5.

 

Wannan na zuwane bayan kullen makarantu da aka yi dalilin zuwan Cutar Coronavirus/COVID-19 a shekarar data gabata.

 

Jihohin Katsina, Sokoto, Zamfara, Nija, Jigawa,  Kano, da Yobe na cikin wanda suka kulle makarantun.

 

Wasu jihohin sun kulle gaba daya makarantun dake yankin da ake fama da matsalar tsaron, yayin da wasu suka kulle iya makarantun Kwana kawai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *