fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Jirgin Emirates ya ɗage haramcin daina jigilar fasinjojin Najeriya zuwa Dubai

Wata biyar bayan haramta jigilar fasinjoji daga Najeriya zuwa ƙasar, hadaddiyar daular larabawa wato UAE ta dage haramcin daga ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta.

Kamfanin Emirates ya sanar a shafinsa na intanet cewa mahukuntan UAE sun sanar da cewa daga 5 ga watan Agusta 2021, matafiya daga Najeriya da wasu ƙasashen 10 da haramcin ya shafa za su ke shige da fice a ƙasar.

Ƙasashen sun ƙunshi India da Pakistan da Sri Lanka da Uganda da Vietnam da Afirka ta Kudu, da Afghanistan da Indonesia, Bangladesh da Nepal.

Emirates a wani gajeren sakonsa ya ce, “Za mu wallafa bayanai kan sabbin sharudanmu da ka’idoji kan tafiye-tafiye, nan ba da jimawa ba.”

Tun a watan Maris din wannan shekarar nan, aka daina balaguron fasinjojin tsakanin Najeriya da UAE saboda rashin jituwar da ya biyo baya kan matakan kariya daga annobar korona.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *