fbpx
Friday, May 14
Shadow

Jiya Najeriya ta gamu da tashin hankali da aka dade ba’a ga irinshi ba>>Bukola Saraki

Tsohon kakakin majalisar Dattijai Bukola Saraki ya bayyana cewa a jiya, Najeriya ta gamu da tashe-tashen hankula da aka dade ba’a ga irinsu ba.

 

Yace daga Kaduna zuwa Yobe zuwa Legas, an samu rahotanni n matasalar tsaro da basu da dadi.

 

Yace an samu Rahoton kafa tutar Boko Haram a karamar Hukumar Shiroro dake jihar Naija. Inda nan ne cibiyar babbar tashar samar da wutar Lantarkin Najeriya, kuma duka-duka Kilometers 2 zuwa babban birnin tarayya, Abuja.

 

Yace kuma an samu rahoton kai hare-haren Boko Haram a garin Mainok inda suka rika farwa jama’ar gari da kuma Sojoji.

 

Yace a jihar Kaduna kuma an samu Rahoton kashe daliban jami’ar Greenfield da ‘yan bindigar suka sace. Yace hakanan kuma an sace daliban jami’ar koyon ilimin harkar Noma a Makurdi dake jihar Benue.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *