fbpx
Thursday, July 29
Shadow

June 12: Matasan Naija Delta, Dana Arewa da Kungiyar Daliban Najeriya sun ce ba zasu yi Zanga-Zangar ba

Wasu matasan yankun Naija Delta sun bayyana cewa, ba zasu shiga a yi Zanga-Zangar June 12 dasu ba.

 

Wasu kungiyoyin fafutuka dai sun bayyana aniyarsu ta fara Zanga-Zangar a yau, June 12 ranar Dimokradiyya wadda suka ce zasu nuna bacin ransu kan matsalolin da suka baibaye Najeriya, amma jami’an tsaro sun yi barazanar hana Zanga-Zangar.

 

Hakanan itama kungiyar Daliban Najeriya,  NANS wadda da farko ta so a yi Zanga-Zangar da ita, ta janye daga Zanga-Zangar inda ta bayyana cewa, bata tare da masu kiran a sauke shugaba Buhati daga Mulki.

 

Itama dai kungiyar matasan Arewa ta nesanta kanta da lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *