fbpx
Friday, May 14
Shadow

Ka bani hakuri, ‘Yan Bindiga zasu iya kasheka>>Fr. Mbaka ya gayawa Garba Shehu

Babban malamin Addinin kirista,  Rev. Fr. Ejike Mbaka ya mayarwa da fadar Gwamnatin tarayya martani kan cewa ya nemi a bashi kwangila ne aka ki shiyasa yake cacakar gwamnatin Shugaban kasar.

 

Mbaka ya goyi bayan Shugaban masa, Muhammadu Buhari a zabukan 2015 da 2019, saidai Kwatsam, kwanannan sai aka jishi yana bayyana cewa kamata yayi Shugaban kasar ya sauka ko kuma majalisa ta tsigeshi.

 

A martaninsa ga wancan zargi da Fadar Shugaban kasa ta masa ta bakin Garba Shehu,Mbaka a yayin da yakewa mutanen cocinsa jawabi yace abin dariyane da wasan Yara.

 

Yace dalilin da yasa bai yi maganaba,yana jiran a Masa Wahayi ne, yace kuma duk wanda ke inkarin maganarsa to ya kiyayi kansa dan kuwa maganar Me tsawane.

 

Yace mutane 3 da aka ce ya je dasu fadar Shugaban kasa, sun ce zasu iya kawo karshen matsalar tsaro dan habbaka tattalin arzikin Najeriya ne inda suka nemi ya musu jagoranci zuwa ganin Shugaban kasar.

 

Yace kumama Shin wadanda ake baiwa Kwangilar sun Fishine? Yace kuma Hakan ya nuna Gwamnatin basa sakawa mutum idan ya musu abin arziki.

 

Yace bai kamata ace wannan gwamnati ta yi fada dashi ba. Ya kara da cewa,kamata yayi Garba Shehu ya bashi Hakuri dan ‘yan Bindiga zasu iya kasheshi, yace idan lamari ya baci, duk jami’an tsaron dake tare dashi ba zasu iya bashi kariya ba.

“Anyone who says the truth is branded a terrorist.

“Are those given contracts better than me? They have shown that they don’t have a reward mechanism.

“The last person this administration should fight is Fr Mbaka.” He said.

 

“Garba Shehu that is talking, the bandits can kill him too. No amount of security can save them if things get worse.

“They have shown they don’t have reward mechanism. Shehu should be apologising to me.

“They are busy branding communities and states terrorists. If Kaduna, Benue, and other places are branded terrorist states, will Nigeria not be branded a terrorist country?”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *