fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Ka gaya mana sunan wanda suka sace dalibai da kace ka sani in kuma ba haka ba to da hannunka>>ACF ta Gwamna Matawalle

Kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF ta bayyana cewa Gwamna Matawalle ya fito ya bayyana sunayen wanda yace ya sani da suka sace daliban makarantar Jangebe.

 

Gwamna Matawalle a lokacin da Sarakunan Jihar Zamfara suka kai masa ziyarar jaje kan satar daliban, ya bayyana cewa idan ya fadi sunan wanda suka sace daliban, ‘yan Najeriya zasu sha Mamaki.

 

Sannan kuma ya bayyana cewa wasu sun baiwa ‘yan Bindigar kudi dan kada su saki daliban.

 

A martaninta, ACF ta bakin shugabanta, Audu Ogbe a sanarwar da kakakin,  Emmanuel Yawe ya fitar tace gwamnan ya fito ya fadi sunan wanda suka sace daliban, in kuma ba haka ba, Jami’an tsaro su tuhume shi da hannu a lamarin.

 

Kungiyar tace kalaman na Gwamnan sun basu kunya dama yankin Arewa gaba daya.

 

“The Arewa Consultative Forum ACF is stunned by a statement accredited to the Zamfara Governor, Bello Matawalle.

“The governor is reported in the media to have told 17 Emirs who paid a sympathy visit to him on the kidnap of 317 school girls from Government Girls Secondary School Jangebe in Talata Mafara that he knew the identity of the kidnappers & if he revealed their identity, Nigerians will be shocked.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *