fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Ka tabbatar an saki Nnamdi Kanu cikin lafiya – Ministan Shari’a na kasar Kanada, Madu ya fada wa AG Malami

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Alberta, Kanada, Kelechi Madu ya nemi Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta saki shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu cikin aminci.

Idan zaku tuna gwamnatin tarayya ta kama Kanu kamar yadda babban lauyan Najeriya Malami ya sanar a watan da ya gabata 28 ga Yuni.

Lauyan Kanu, Ifeanyi Ejiofor, ya ce rundunar ‘yan sanda ta musamman ta Kenya ce ta kame shi tare da azabtar da shi kafin a mika shi ga gwamnatin Najeriya, amma gwamnatin Kenya ta musanta cewa tana da hannu.

Yanzu haka Madu ya fito ya yi Allah wadai da gwamnatin tarayya sannan ya nemi kasashen Burtaniya, EU, Amurka, Isra’ila, Kanada da Jamus da su yi amfani da dukkan karfinsu, gami da diflomasiyya, don tabbatar da tsaro da sakin Mazi Nnamdi Kanu.

A karshen ya gargadi Gwamnatin Tarayya Nageriya da tayi abunda ya dace domin kare hakkin yan kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *