fbpx
Friday, May 14
Shadow

Kada ku yadda a hure muku kunne kan raba Kasa>>Osinbajo da Sultan suka gayawa ‘yan Najeriya

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad na III sun jawo hankalin ‘yan Najeriya da cewa, kada su yadda da masu kiran a raba kasa.

 

Sun bayyana cewa ya kamata a mayar da hankali wajan koyar da matasa tarihin Najeriya. Sun bayyana hakane a wajan bikin kaddamar da wani Littafi dake magana akan Tarihin Musulunci a kasar YarbaWa.

 

Kungiyar Yarbawa Musulmai, MUSWEN ce ta samar da Littafin. Osinbajo yace masu neman a raba Najeriya yawan cinsu basu da cikakken ilimin abinda suke yi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *