fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Kaftin din Sifaniya, Sergio Busquets ya kamu da cutar sarkewar numfashi ana sauran kwanki biyar a fara buga gasar Euro

Hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Sifaniya (RFEF) ta tabbatar a ranar lahadi cewa dan wasan tsakiya na Barcelona, Sergio Busquets ya bar sansanin su na atisayi Las Rozars bayan ya kamu da cutar sarkewar numfashi.

Yayin da su kuma sauran yan tawagar gabadayan sakamakon gwaji ya nuna cewa basa dauke da cutar, kwanaki biyu bayan sun tashi wasa da kunnen doki tsakanin su da Portugal 0-0.

Sifaniya zata kara da Lithuania a Lenages ranar talata wanda zai kasance wasanta na sada zumunta na karshe kafin a fara buga Euro, amma dole zata dauko wasu yan wasa daga tawagar yan wasan ta masu kasa da shekaru 21 saboda tabi dokar kiwon lafiya.

Kocin tawagar yan wasan Sifaniya masu kasa da shekaru 21 Luis De La Fuente ne zai jagoranci wasan a madadin kocin babban tawagar kasar Luis Enrique a cewar hukumar ta (RFEF).

 

Sergio Busquets: Spain captain tests positive for Covid-19 five days before Euro 2020 start

The Spanish Football Federation (RFEF) confirmed on Sunday the Barcelona midfielder has left their Las Rozas training camp after posting a positive result in the latest round of testing.

However, the rest of the team all posted negative results two days after their 0-0 draw against Portugal in Madrid.

Spain take on Lithuania in Leganes on Tuesday in their last warm-up game before the European Championship, but they will now be forced to field players from their U21 side to follow strict health protocols.

Spain U21 boss Luis De La Fuente will also take charge of the team instead of the senior team’s head coach Luis Enrique, said a RFEF statement.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *