fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Kafun Na Sauka A Mulki, Zan Kafa Tarihin Da Ba’a Taba Kafa Irin Sa Ba A Nijeriya, Cewar Shugaba Buhari

Daga Comr Abba Sani Pantami

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai rufe gibin kayayyakin more rayuwa a kasar kafin ya sauka a mulki, wanda hakan zaisa ya kafa wani tarihi da ba a taba ba Nijeriya, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Ya kara da cewa, sabanin gwamnatocin baya, za a yi amfani da rancen da gwamnatinsa ta karbo wajen gudanar da ayyuka domin rage yawan gibin ababen more rayuwa a kasar nan.

Shugaban ya yi magana ne ta bakin shugaban ma’aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, a wajen bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Afirka, Dokta Bamanga Tukur mai taken ‘Legacies of a Legend’ a Abuja.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *