fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Kai Duniya: An kama wata mata dake kaiwa ‘yan Bindiga ‘ya’yanta mata a Kaduna suna lalata dasu

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, an kama wata mata dake kaiwa ‘yan Bindiga Karuwai.

 

Hukumar ‘yansanda ce ta kama matar wadda ake zargi da kaiwa ‘yan Bindigar dake dajin Galadimawa, karamar  hukumar Giwa Karuwai.

 

Maryam Abubakar ta amsa laifinta inda tace tana kai hadda diyarta da ‘ya’yan ‘yan uwanta da sauran ‘yan mata wajan ‘yan Bindigar dan su yi lalata dasu.

 

Hakanan itama wata matashiya, Fatima Jibrin da saurayinta an kamasu suna kaiwa ‘yan Bindigar karuwai.

 

Ita kuma wata me suna Jummai Ibrahim an kamata ne da cewa tana kai kanta wajan shugaban ‘yan Bindigar yana lalata da ita.

 

Tace tana hakan ne dan ta kare ‘ya’yanta da mahaifinta wanda ‘yan Bindigar suka sha alwashin kashewa.

 

Saidai duka matan sun bayyana nadama akan abubuwan da suke aikatawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *