fbpx
Monday, October 25
Shadow

Kaikai ya fara komawa kan mashekiya: Ji Abinda ‘yan IPOB sukawa wani gwamnan kudu

Yan bindiga sun kai hari ga jerin motocin gwamna Willie Obiano na Anambra tare da tsare su na tsawon awa daya.

A na zargin kungiyar yan awaren Biafra ta IPOB da kai harin, a lokacin da suka tarwatsa taron kamfe da jam’iyyar APGA ta shirya a makarantar sakandaren Otada da ke karamar hukumar Ihiala yau Talata.

Kamar yadda wani mazauni garin ya shaida wa Jaridar Daily Trust, ayarin gwamnan ya shafe awa daya hannun IPOB, kuma an rika jin harbe-harbe a lokacin da su ke tsare da tawagar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda a jihar Anambra DSP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da cewa an kai hari a karamar hukumar Ihiala.

A sanarwar da jami’in ya fitar ya ce rundunarsu ta dakile harin da a ka kai a Otada, inda ta kwato makamai da motoci a hannun maharan.

A martanin da gwamnati ta mayar ta hannun kwamishinan yada labarai C.Don Adunuba, ta ce jami’an tsaro sun yi namijin kokari wurin dakile harin bayan musayar wuta da maharan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *