fbpx
Monday, September 27
Shadow

Kalli Barawon da ya je sata Masallaci amma bacci ya kwasheshi har aka kamashi a jihar Kebbi

Wani da ake zargin Barawone ya balla masallaci ya shiga yayi sata a jihar Kebbi amma kuma sai sa’a ta kare masa inda bacci ya kwasheshi.

 

An kama Hamza Usman dan shekaru 31 a Kauyen Bayan Kara ranar Juma’a, 30 ga watan Afrilu na shekarar 2021.

 

Wanda aka kama ya amsa laifinsa inda yace, ya saba shiga gidajen mutane dan satar waya idan sun yi bacci. An kamashi a masallacinne bayan da mutane suka fito yin Sallar Asuba.

 

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *