fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Kalli bidiyon yanda ‘yan Bindiga suka tare hanyar Abuja zuwa Kaduna, dandazon jama’a na gudun neman tsira, sojoji ma sun tsere

Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama tarkon masu garkuwa da mutane inda suke cin karensu da tsakar rana.

 

A kwanakin baya an dan samu saukin Lamarin amma yanzu abin ya dawo gadan-gadan inda ‘yan Bindigar ke sace mutane son ransu.

 

Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya fitar da wannan Bidiyon inda aka ga mutane na ta gudu dan tsira da ransu daga hannun ‘yan Bindigar.

 

A cikin bidiyon za’a iya jin yanda me daukar bidiyon ke cewa wani soja ya yadda mashin dinsa ya tsere  hakanan wasu na cewa sojojin ma sun tsere.

 

Dan kallon Bidiyon, danna nan

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *