fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Kalli hoton matar data shekara 40 bata yi bacci ba

Wata mata me suna Li Zhanying ta bayyana cewa tun tana da shekara 5 rabonta da bacci.

 

Matar ta fitone daga kasar China kuma wannan ikirari nata ya baiwa Likitoci mamaki sosai.

 

Rahoton yace makwabtanta da dama sun so su kureta akan cewa bata bacci amma da an fara sai kowa ya buge da bacci amma ita tana nan kuri ido biyu.

 

Matar ta rika shan maganin bacci amma duk a banza, bai mata magani ba.

 

Mijin matar ma ya tabbatar da wannan ikirarin inda yace tunda suka yi aure matar tasa bata bacci.

 

Saidai Likitoci a Beijing sun samar mata da maslaha inda a yanzu take samun baccin minti 10.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *