fbpx
Monday, November 29
Shadow

Kalli Hotuna: Wata mata ta sayi Atamfofi na Dubu Dari amma wannan matashin ya aika mata da gidan Sauro

DAMFARA: Ta Yi Odar Atamfofi Na Dubu Dari Ya Aiko Mata Da Gidan Sauro A Kunshe

Daga Aliyu Ahmad

Wani matashi mai suna Aliyu Hussani Salisu, wanda ya kware wajen damfarar mutane ta kafafun sadarwa ya shiga komar ‘yan sandan jihar Kano, bisa zarginsa da damfarar al’umma da sunan zai sayar musu da atamfofi, leshi, shaddodi da sauransu.

Dubun sa ta cika ne a yayin da ya damfari wata mata daga garin Yelwan Shendam dake jihar Filato, bayan sun yi cinikin kaya na naira dubu dari, inda ta tura masa da kudin, shi kuma ya je tashar Unguwa Uku ya aiko mata da kayan, inda bayan ta karbasai ta kunshin gidan sauro ne.

Bayan ta mika korafin ta ga jami’an ‘yan sandan jihar Kano ne sai aka bazama nemansa, inda aka yi nasarar kama matashin wanda dan unvuwar Hotoro ne.

An kama shi ne dauke da na’urar kwamfutar tafi da gidanka (laptop) a yayin da yake shirin damfarar wasu mutanen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *