fbpx
Monday, September 27
Shadow

Kalli mota me dauke da kayan Miliyan 30 dake kan hanyar zuwa Arewa da ‘yan IPOB suka kone kurmus

Tsageran da ake zargin ‘yan IPOB ne sun kone wata mota kurmus dake kan hanyar zuwa Kogi.

 

Motar na dauke da kayan gyaran motane da darajarsu ta kai Naira Miliyan 30.

 

Lamarin ya farune a Nsukka dake jihar Enugu ranar Litinin.  IPOB dai sun saka dokar hana fita ruk ranar Litinin saboda ci gaba da tsare shugabansu, Nnamdi Kanu da jami’an tsaron Najeriya ke yi.

 

Direban motar, Fabian Eze ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN cewa, ya taso ne daga Nnewi a daren ranar Lahadi, amma ya tsaya saboda tsoron IPOB kada su kai masa hari.

 

Yace sun je cin abinci kawai sai suka ga mutane na gudu suna fadin cewa an bankawa motar dake bakin titi wuta. Yace shi da yaron motarsa sun je wajan motar inda suka ga komai ya kone ciki hadda kudin su sama da 200,000.

 

Yace bai san yadda zai yi ba, ko masu kayan da me motar zasu ce sai ya biyasu?

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Mr. Daniel Ndukwe ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa, suna kan bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *