fbpx
Friday, May 14
Shadow

Kalli takardar da Boko Haram suka rika rabawa jama’ar Garin Geidam na jihar Yobe, Sun yanke Sabis din Wayar hannu ta garin

Jama’ar garin Geidam na jihar Yobe wanda canne mahaifar shugaban ‘yansandan Najeriya Baba Usman a yanzu basa da damar amfani da layukan wayarsu.

 

Dalili Kuwa Boko Haram ta lalata Sabis din Layukan wutar garin na MTN dana Airtel. Garin dai kuma shine mahaifar tsohon Gwamnan jihar, Ibrahim Geidam.

 

Boko Haram sun fara kai hari garin da yammacin jiya, Juma’a, inda daga baya Jirgin yakin Sojojin Najeriya ya korasu, amma bayan ya wuce, sai suka dawo.

 

Wani me suna Ali Maina ya bayyana cewa, Boko Haram din na fasa shaguna suna kwasar kaya kuma suna da Motocin Hilux kusan 15, yace akwai bukatar Sojoji su kara kaimi.

 

Sun kuma rabawa jama’ar garin takarda me dauke da bayanin cewa suna yaki ne da Sojojin Najeriya saboda Jihadi dan kafa daular Musulunci.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *