fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Kalli yanda Motar giya ta faɗi daf da ofishin Hisba a Kano

Motar giya ta faɗi daf da ofishin Hisba a Kano

Wata mota maƙare da katan-katan na giya ta faɗi a daidai ofishin Hisba na Panshekara, Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa kawai gani a ka yi motar, ƙirar Hilux, ta afka cikin kwata.

Bayan da mutane su ka kai agaji ne, sai su ka ga ashe motar barasa ce, inda gurin ya gurmuɗe da tsamin giya.

An dai yi ƙoƙarin zaro direban motar wanda ya ji ciwuka, yayin da kwalaben giyar da dama ne su ka faffashe.

Kawo yanzu dai Hisba ba ta ce komai kan batun ba.

Daga Daily Nigerian.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *