fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Kalli yanda Wani Fasto ya gyara tsohon Masallaci ya dawo sabo

Wani Fasto me suna Oluwaseun Alabi dake jihar Osun yayi abin gwaninta da ake ta yaba masa.

 

Duk da yake Kirista, ya gyara wani tsohon masallaci ne inda ya dawo sabo gwanin ban sha’awa.

 

Masallacin na yankin Ikire na jihar ne inda aka ruwaito cewa ya kai wajan shekaru 60 da ginawa.

 

Faston dai ya bayyana cewa lokacin suna yara, tare suke wasa da musulmai na unguwarsu. Wani me suna Bakara Adegboyega ne ya wallafa hotunan lamarin a shafinsa na Facebook.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *