fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Kamar Zamfara, gwamnatin Najeriya ta rufe sabis na sadarwa a Katsina

Kamfanonin sadarwa sun rufe sabis na GSM a akalla kananan hukumomi 13 na jihar Katsina.

A ranar 3 ga watan Satumba, Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, ta ba da umarni ga kamfanonin sadarwa da su rufe ayyukan su a jihar Zamfara don shawo kan matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar jihar.

Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, Kananan hukumomin da abin ya shafa su ne Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma da Kurfi wadanda ke kan iyakar dajin Ruggu inda mafi yawan ‘yan fashin ke buya. Sauran ukun sun hada da Funtua, Bakori da Malumfashi.

Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da NCC ta musanta shirin rufe tashoshin sadarwa a Katsina.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *