fbpx
Monday, November 29
Shadow

Kamfanin NNPC zai kashe biliyan N621 wajen gyaran manyan hanyoyi 16

Kamfanin Man Fetur na Najeriya ya kuduri aniyar kashe biliyan N621 wajen gyaran hanya, biyo bayan dakatar da yajin aikin da Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Kasa ta yi.

An ba da rahoton cewa NUPENG ta yi barazanar direbobin tankar man fetur za su fara yajin aiki a ranar 11 ga Oktoba saboda mummunan halin manyan hanyoyin kasar da sauran batutuwa.

Amma daga baya an dakatar da shirin yajin aikin bayan da kungiyar kwadago da mahukuntan NNPC suka samu fahimtar juna a wani taro da aka gudanar a Ibadan, jihar Oyo a ranar 10 ga watan Oktoba.

Kungiyar kwadagon ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen fara yajin aikin ba tare da wani sanarwa ba idan har ba a cika aiwatar da fahimtar da aka samu a taron ba cikin lokacin da aka amince.

A cewar wata takarda, gudanarwar NNPC ta yanke shawarar yayin taron don samar da kudin gyaran wasu muhimman hanyoyi ta hanyar tsarin biyan harajin ababen more rayuwa na hanyar haɗin gwiwa tare da Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya da Ma’aikatar Haraji ta Tarayya don gyara sassan tituna 16 a kimanin kudi biliyan N621.

Hanyoyin da za a gyara su, duk da haka, ba a ambaci su a cikin takardar ba.

Shirin Ba da Lamuni na Harajin na Hanyoyi wani yunƙuri ne na Gwamnatin Tarayya wanda ke ba da dama ga kamfanoni masu zaman kansu su shiga cikin aikin hanyoyi don musanya kuɗin haraji.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *