fbpx
Monday, May 10
Shadow

Kamfanin Siminti na Dangote Zai Biya Kudin Harajin Biliyan N40 a Zangon Farko Na Wannan Shekerar

Kamfanin simintin Dangote ana sa ran zai biya Naira biliyan 40.39 na haraji ga Najeriya daga sakamakon aikinsa a zangon farko na shekarar 2021, in ji kamfanin a jiya.

A cikin wata sanarwa, kamfanin da ke yin siminti ya ambaci sakamakonsa na kudi da aka samu a ranar Juma’a, 30 ga Afrilu, 2021, inda ya bayyana cewa kudin kai a biya harajin kamfanoni a lokacin da ya kare daga 31 ga Maris, 2021.
Adadin haraji ya karu da kashi 47.3 bisa dari a wannan kwata fiye da biliyan N27.42 da aka biya a bara, 2020.
Kamfanin Siminti na Dangote a yanzu haka yana biyan gwamnati haraji na VAT miliyan N240 a kullum, wanda hakan yasa ta zama daya daga cikin manyan masu biyan haraji daga kamfanoni masu zaman kansu, kamar yadda ta bayyana.
Kamfanin ya kuma ce ya zabi samar da kudade domin gina manyan hanyoyi a jihohin Legas da Kogi. “Hanyoyin sune babbar hanyar Port Apapa da ke zuwa tsohuwar kofar shiga da kuma hanyar Lokoja-Obajana-Kabba wacce ta bi ta jihohin Kogi da Kwara.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *