fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Kamun da EFCC sukawa Bukola Saraki ya dameni, akwai yiyuwar ana son hanashi takarane a 2023>Tanko Yakasai

Uban kasa kuma dattijo daga jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa, sam bai ji dadin kamun da akawa Tsohon Kakakin majalisar Dattijai,  Bukola Saraki ba.

 

Ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai a Kano, kamar yanda PMnews ta ruwaito.

 

Tanko Yakasai ya bayyana cewa, Bukola Saraki Dansa ne, saboda Mahaifinsa abokinshi ne, sannan shima Bukola Sarakin Abokin babban dansane.

 

Yace dan haka dole abinda aka masa ya dameshi, yace lallai ba zai yiwa hukuma katsalandan kan aikinta ba amma wannan alamu ne dake nuna ana son hana Bukola Saraki tsayawa takara a 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *