fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Kananan yara 2 ne suka kone a gobarar data tashi a wani gida dake jihar Naija

Kananan yara 2 ne suka rasa rayukansu a wata gobara data tashi a Anguwar Dawaki dake Suleja.

 

Yaran, Suraiya da me shekaru 7 da kuma Habib me shekaru 9 sun kone kuma suka mutu a gobarar kamar yanda Daily Trust tau ruwaito.

 

Mahaifin yaran, Alhassan Jibrin Yanci yayi kokarin cetosu amma abin ya gagara inda shima da kyar yasha da kuna a jikinsa, kuma yana Asibiti ana dubashi.

 

Wani Mazaunin Yankin da abin ya faru a idonsa Bashir Ibrahim ya bayyanawa manema labarai cewa, da misalin karfe 3 na daren juma’a ne abin ya faru kuma mahaifiyar yaran bata nan saidai mahaifinsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *