fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Yanda Kankana ke taimakawa karfin gaba, Maganin Hawan Jini da sauransu

Kankana na daya daga cikin jerin kayan itatuwa masu zaki da kuma al’fanu ga lafiyar jikin Dan Adam.
Wani abin da zai ba ka mamaki shi ne ba duk masana ne suka amince da cewa kankana dan bishiya ce ba, wasu daga cikin manya-manyan masu bincike suna ganin cewa ana sakata a cikin ganyayyaki ne kamar su Cucumber sai dai tana da zaki, ana samunta a ko’ina cikin nau’uka da launuka mabambanta, wanda har jami’ar Washington da ke Amurka ta fitar da wasu alkaluma inda take cewa akwai nau’o’in kankana a duniya har 126 dukkansu suna dauke ne da nau’o’i kala daban-daban.
Kankana wacce ake mata lakabi da uwar ruwa tafi amfani ne a lokacin da ta nuna sosai masana sun ce sinadaran nunannar ya fi taruwa sosai musamman beta-carotene dake cunkushe a cikin jan tozon nan wanda ke matukar taimaka ma idanu.
Kankana ta kan taimaka wa koda matuka, domin ruwan da ke cikinta, kamar dai yadda aka sani takan saukake wa taruwar fitsari da fitarsa, wannan sabo da tana da sinadarin Potassium wanda ya ke taimakawa wajen korar gurbataccen sinadari daga jukkunammu, sannan sinadarin yana rage yawan sinadarin Hyperuricemia a cikin jini.
 Zakin cikinta kuma na ba mutum karfi, tana kuma kara ma jiki ruwa.
Nunannar kankana na taimaka ma fata saboda sinadarin lycopene dinta.
Sinadarin arginine dake cikinta na kara yawan nitric oxide dake kara ma namiji karfin gaba.
Hakanan Nitric oxide da wasu sinadaren kankana na taimakon masu ciwon zuciya da hawan jini.
kankana Tana haifar da samuwar wadataccen barci.
Sinadarin vitamin C dinta na taimako wajen maganin cututtuka da dama.
Tana maganin ciwon daji kala-kala, da kuma ciwon koda.
Tana da sinadarai masu kara karfin kashi (bone) da kuma maganin kumburin jiki musamman gabban jiki (joints).

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *