fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Karawa Magu girma ya nuna cewa kana goyon bayan cin hanci>>PDP ga shugaba Buhari

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta bayyanawa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa karawa tsohon Shugaban EFCC girma cin zarafin ‘yan Najeriya ne.

 

PDP ta bakin kakakinta, Kola Ologbondiyan ta bayyana cewa, sam hakan bai dace ba kuma yana nuna cewa, Gwamnatin na goyon bayan cin hanci.

 

A jiyane dai Rahotanni suka bayyana cewa, Gwamnatin tarayya na shirin yiwa Magu karin girma zuwa AIG.

 

A baya dai bayan saukeshi daga mukamin shugaban EFCC, kwamitin Ayo Salami ya bayar da shawarar cewa, a hukunta Magu kan laifukan da ake zarginsa dasu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *