fbpx
Monday, November 29
Shadow

Karfin soji ba zai samar da zaman lafiya ba-Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce tarin makaman nukilya da bindigogi ba shi ne zai samar da zaman lafiya a duniya ba.

Mr Jonathan, wanda ya bayyana haka ranar Litinin a wurin wani taron kasashen duniya mai taken World Summit 2020 a birnin Seoul na Koriya ta Kudu, ya kara da cewa zaman lafiyar duniya “yana samuwa ne a cikin zukatanmu.”
“Ya kamata mu binciki zukatanmu sannan ko da yaushe mu nuna so da kauna domin kare mutanenmu.”
Tsohon shugaban na Najeriya ya sha yabo sosai lokacin da ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasa na 2015, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *