fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Karin bayani kan wayar Salula ta farko a Najeriya: Menene sunan wayar, Nawa ake sayar da ita, dame dame ta ke yi, a Aina za’a sameta?

A yaune aka gabatarwa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari sabuwar wayar Salula ta farko da aka kera a Najeriya.

 

Kamin wannan lokaci, Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa, an fara kera wayar hannu a Najeriya da kuma Sim din wayar, Abinda ya jawo cece-kuce sosai.

 

Saidai gabatarwa da shugaba Buhari wayar a yau ta tabbatar da maganar Ministan.

 

Menene Sunan wayat?

 

Sunan wayar ITF Mobile

 

Nawane Farashinta, sannan kuma a ina za’a sameta?

 

Hukumar bayar da horo akan fasaha ta ITF ce ta samar da wayar, Zuwa yanzu dai ba’a bayyana cewa ko an saka wayar a kasuwa ba ballantana a san farashinta.

 

Dame-Dame ta ke yi?

 

Hakanan babu cikakken bayanin abubuwan wayar da take, ba kamar yanda aka saba sakin wayoyin hannu a kasashen Duniya ba, inda kamin ma a saki wayar zaka san irin amfanin da take da kuma farashinta da inda za’a iya samunta, ITF Mobile zuwa yanzu bata ba’a fitar da cikakken bayaninta ba.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *