fbpx
Friday, May 14
Shadow

Karin Kudin makaranta Nunki 6 ya dagawa daliban Jami’ar Kaduna hankali, Da yawa zasu hakura da karatun

Daliban jami’ar Jihar Kaduna sun bayyana rashin jin dadinsu bayan da suka wayi gari suka ga karin kudin makaranta da aka musu na nunki 6.

 

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar Makarantar ta karawa daliban jihar  ma wanda ba ‘yan Asalin jihar ba kudi.

 

A baya dai, dalibai wandaa ‘yan Asalin jihar ne dake tsangayar Art suna biyan 23,000 sai kuma wanda ke bangaren Science suna biya 27,000. Wanda kuma ba ‘yan Asalin jihar bane suna biyan 33,000 da 37,000.

 

Saidai a sabon karin da aka yi, dalibai da ba ‘yan jihar ba zasu biya dubu dari biyar, watau, 500,000 wanda kuma ‘yan jiha ne zasu biya 300,000.

 

Abdullahi Yakubu Isa me magana da yawun daliban jami’ar ya bayyana cewa hankalim dalibai da yawa ya tashi, inda yace amma suna kan tuntuba dan tabbatarwa.

 

Yace idan dai hakan ta tabbata to lallai dalibai da yawa dole saidai su jingine karatun nasu, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

 

Saidai kokarin jin ta Bakin kakakin makarantar ya faskara inda yace zai nemi ‘yan jaridar amma bai yi ba.

 

Amma Shugaban jami’ar, Farfesa Abdullahi Ashafa ya tabbatar da karin kudin makarantar inda yace an yi hakanne dan samarwa daliban ingantaccen ilimi da zasu zama masu amfani a cikin al’umma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *