fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Karshe Korona: Gwamnatin Amurka ta ce Amurkawa da akayi wa rigakafin Covid-19 na iya cigaba da rayuwarsu ba tare da takunkumi ba

Cibiyar Kula da Cututtuka a Amurka ta sanar da cewa Amurkawa masu cikakken rigakafin Covid-19 za su iya cigaba da rayuwarsu ba tare da takunkumi ba (Face mask).

Daraktan CDC, Rochelle Walensky ce ta bayyana hakan a wani jawabi da aka yi a fadar White House a ranar Alhamis 13 ga Mayu.

Walensky ta ce, “Idan kana da cikakkiyar riga-kafin Covid-19, za ka iya fara yin abubuwan da ka daina yi a baya saboda annobar.

Walensky ta ce “Dukkanmu mun dade muna son wannan lokacin da za mu iya komawa cikin harkokin mu na yau da kullun.”

Sanarwar ta zo ne bayan an caccaki Walensky ya game yin jinkiri wajen baiwa jama’a damar cigaba da yin harkokin su na yau da kullum ba tare da wata takura ba.

Sai dai a karshe tace dole ne masu tafiya a cikin bas, jiragen ƙasa, jiragen sama su sanya takunkumin a lokacin da suke tafiya.

Shugaba Joe Bide yayi maraba da wannan umurnin, tare da bayyana wannan a matsayin lokacin farin ciki ga Amurkawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *