fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Karya ‘yansanda suke mana, ba mu muka kashe musu jami’i ba>>’Yan Shi’a

Kungiyar IMN da aka fi sani da Shi’a ta karyata hukumar ‘yansanda inda tace ba itace ta kashe jami’in hukumar me suna ASP Ezekiel Adama ba.

 

Kakakin hukumar ‘yansandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ta bayyana cewa,’yan shi’ar a Zanga-Zangar da suka yi ranar Juma’a a Abuja sun kashe Adama. Ta kara da cewa an kama 49 daga cikinsu kuma nan gaba za’a gurfanar dasu gaban kuliya idan an kammala bincike.

 

Saidai kakakin IMN, Ibrahim Musa ya karyata wannan jawabi na ‘yansanda inda yace dama can gwamnati na shirin alakantasu da ta’addanci kuma wannan daya ce daga cikin hanyoyin da ta biyo wajan cimma burinta.

 

Yace dan haka suna kira ga jama’a da su yi watsi da wancan ikirari karyane. Yace sun yi tattakin ranar Qudus lafiya a garuruwa daban-daban na Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *