fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Kasar Amurka ba zata iya sawa a kama Abba Kyari ba tunda ba dan kasar ta bane>>Hukumar ‘yansanda

Hukumar ‘yansandan Najeriya ta bayyana cewa, Kasar Amurka bata da hurumin da zata sa a Kama DCP Abba Kyari tunda ba dan kasarta bane.

 

PSC ta bayyana cewa, Najeriya kasa ce me cin gashin kanta wanda kuma tana da dokokinta dan haka abin mamaki ne ace kotu daga kasar Amurka zata bata umarni.

 

Hukumar ta kara da cewa babu wata bukatar kama Abba Kyari a hukumance da aike mata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *