fbpx
Monday, November 29
Shadow

Kasar Amurka ta kafa sharadin kada a yi amfani da jiragen da ta sayarwa Najeriya wajan kashe ‘yan Bindiga

Rahotanni sun bayyana cewa, Kasar Amurka ta kafawa Najeriya sharadin kada a sake a yi amfani da jiragen da ta sayarwa Najeriya wajan kashe ‘yan Bindiga.

 

Saidai Amurkar tace, ‘yan ta’adda kawai take so a kashe da Jiragen.

 

Shuwagabannin sojojin Najeriya sun aikewa da majalisar tarayya bukatar a basu damar yin amfani da wadannan jirage da ma sauran makamai dan murkushe ‘yan Bindigar dake addabar musamman yankin Arewa maso yamma.

 

Wannan dalili ne yasa Majalisar take neman shugaban masa, Muhammadu Buhari ya saka ‘yan Bindigar cikin jerin ‘yan ta’adda,  kamar yanda Punchng ta ruwaito.

 

Gwamnatin tarayya ta siyo jirage masu kirar A-29 Tucano akan Miliyan $496

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *