fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Kasar Benin Republic ta ki amincewa da gaggauta dawo da Sunday Igboho Najeriya: Ji dalilinta

Kasar Benin Republic da ta kama me ikirarin fafutukar kafa kasar Oduduwa,  Sunday Igboho ta ki amincewa da bukatar Najeriya ta dawo mata da Sunday Igboho cikin gaggawa.

 

Ranar Laraba ne dai Najeriya ta so a dawo mata da Sunday Igboho amma Benin taki inda tace ba zata yadda ayi wani abu da baya bisa doka ba.

 

Wani jami’in tsaro a kasar ya bayyanawa Punchng cewa, Najeriya na son a gaggauta kai mata Sunday Igboho amma su sun kiya.

 

Lauyan Igboho ya bayyana cewa, kasar Benin tace sai an yi shari’a an ga idan Igboho na da laifi ko kuwa baya dashi kamin a yadda a baiwa Najeriya shi.

 

Saisai Gwamnatin tarayya ta ki cewa uffan kan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *