fbpx
Monday, May 10
Shadow

Kasar Canada na neman Zaratan Matasa da zasu zama ‘yan kasarta Daga kasashen Duniya Daban-Daban: Duba Sharudan data saka

Kasar Canada bude hanya ga ‘yan kasashen waje da zasu samu damar zama ‘yan kasar na dindindin.

 

Sabuwar dokar da kasar ta fitar tace zata baiwa ‘yan kasashen waje da sukabyi karatu a jami’o’in kasar su 40,000 damar zama ‘yan kasar.

 

Wannan yana cikin tsarin da Ministan kasar, Marco Mendicino ya fitar na na baiwa ma’aikata masu aiki na musamman 90,000 da kuma wanda suka kamala karatu a kasar da taimakawa tattalin arzikinta damar zama ‘yan kasa.

 

Za’a bude wannan damar nw rana 6 ga watan Mayu har zuwa 5 ga watan Nuwamba na Shekarar 2021.

 

Za’a karbi takardun neman izinin zama kasar daga ma’aikatan lafiya 20,000.

Sai kuma ma’aikata na musaman 30,000.

Sai kuma dalibai 40,000 da suka kamala karatu a jami’o’n kasae da suka fito daga kasashen Duniya Daban-daban.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *